Makomar Leao, Loftus-Cheek, Ake, Rodriguez, Vlachodimos, Toney a kasuwar 'yan kwallo








AC Milan na shirin soma tattaunawa da dan wasan gaba na Portugal Rafeal Leao kuma za ta so ta kulla yarjejeniya kafin gasar cin Kofin Duniya. An alakanta ta da matashin dan shekara 23 kuma suna bibiyar lamarin. (La Gazzetta dello Sport, via Football Italia)


AC Milan na sha'awar sayen dan wasan Chelsea kuma dan wasan tsakiya a Ingila mai shekara 26 Ruben Loftus-Cheek wanda kwantiraginsa da kungiyar zai ci gaba har shekarar 2024. (Calciomercato - in Italian)


Chelsea na gab da kulla yarjejeniya domin nada babban mai daukar ma'aikata na Southampton Joe Shields a matsayin daraktan daukar ma'aikata. (Guardian)


Manchester City ta fada wa kungiyoyi da dama har da Bayern Munich da Inter Milan da suka nemi bayani kan dan wasa Nathan Ake cewa ba za su sayar da matashin mai shekara 27 ba a watan Janairu. (90 Min)


Liverpool tana bibiyar Real Betis kuma dan wasan Argentina Guido Rodriguez, 24 kafin cinikin 'yan wasa a watan Janairu. (Estadio Deportivo - in Spanish)


Rahotanni na cewa Manchester United ta zafafa neman mai tsaron ragar Benfica Odysseas Vlachodimos kuma a shirye suke su saye dan wasan dan shekara 28 wanda Leicester City take nema. (Sportime - in Greek)


Brentford ta bude tattaunawa game da sabuwar kwangila da dan wasan Ingila mai shekara 26 Ivan Toney wanda aka danganta da Tottenham. (Football Insider)


Leeds United na shirin yi wa dan wasan Ingila Jack Harrison wanda Newscatsle ke sha'awarsa a bazara , tayin inganta yarjejeniya. (Football Insider)


Wolverhampton Wanderers sun yi nisa a tattaunawa da tsohon kocin Olympiakos Pedro Martins wanda a baya-bayan nan ya gaza amincewa da wata yarjejeniyar zama kocin Hull City yayin da kungiyar ke hangen nada shi don maye gurbin Bruno Lage. (Maisfutebol)


Kocin Lazio Maurizio Sarri bai ji dadin wasu rahotannin da ke alakanta Dan wasan tsakiyar Serbia Sergej Milinkovic Savic mai shekara 27 da wani yunkuri na zuwa Juventus ba. (Football Italia)

0/Post a Comment/Comments

Breaking News

Ads1

{ads}

Ads2