
Yadda ake turaren wuta na musamman
Turaren wuta ana yin sa ne da itace, domin turara daki, da dukkanin jiki da na tsugunno, da kuma na sutura . Ana zuba shi cikin gaushi ne a kasko. Nan da nan kuwa ka ji kamshi ya gauraye ko ina acikin gida. Daga cikin Itatuwa da ake turare da su kuwa Sun hada da :
Icce Sandal
Icce Hawi
Icce Gab-Gab
Icce Durot
Dadai Sauransu.
Ana yin turare na soyawa Kuma ana yin na jikawa. Ya Danganta Da bukata mutum.
Larabawa da kuma mutane Maiduguri ne su ka fishahara wajen amfani da turare wuta. Mazansu na tai makawa sosai , siyawa matansu turare akai -akai . A wajensu tamkar dole ne amfani da turare . Mace ba ta Dadaraja sai da kasancewa cikin kamshi akoda yaushe .
K AYAN TURARE WUTA
Iccen Hawi
Matan Arewa
Farce
Misik
Alhaji Abdullahi
Salama lekum
Sasora bi a
20 fragrances
Madara turare ( 8)
YADDA AKE HADAWA
Za’a sa iccen Hawi a turmi a daddaka shi sama-sama.
Asa iccen gab-gab shima haka. Sai a juye su cikin mazu bi .
A dauko ruwa n turare Matan Arewa a zuba a kan itatuwa.
A juye Soyayye farce . A zuba Misik. Sai adauko tur aruka :
Alhaji Abdullahi, da salama lekum, da Sasora bi a, da 20
fragrances. Kowanne a bude a juye. Sai Kuma a dauko Madarar turare masu matukar kamshi a zuba su.
A juya da kyau ko ina ya samu ya hade . A samu mazu bi ajuye aciki. Kuma arufe shi sosai .
TURAREN SIKARI
Ruwan turare ( alcohol)
Yara -yara gwangwani 1
Sikari kwano
Kala
Filabo
Madarori Turare 5
YADDA AKE HADAWA
A juye Sikari acikin mazubi . A juye Yara -yara , a sa
madarori turare 5. Sai asa kala ayi ta juyawa h ar sai ko ina
ya hade jikinsa sosai .
Shima wannan turare acikin gaushi ake sawa a turara daki
da shi .
A karshe dai amfani da turare ya kewaye dukkan kasashe .
Haka kuma da sauran jihohi. Ya Kuma can canci ace yana cikin kasafi wata-wata na kowanne Mai gida. Gidanka
kamshi Kuma jikin matarka kamshi. Haka z ai sa ma Ma’ aura ta natsuwa da samun shakuwa da juna.
Post a Comment