YADDA AKE ISTIKHARA (ISTAHARA).


YADDA AKE ISTIKHARA (ISTAHARA)



Kai sallah raka'a 2 kowace raka'a fatiha da sura, a tahiyar karshe wato ta (2)bayan ka gama karatun tahiyar sai kayi salatin Annabi saw sai ka karanta wannan addu'ar Kamar haka

(ﺍﻟﻠﻬﻢ ﺇﻧﻲ ﺃﺳﺘﺨﻴﺮﻙ ﺑﻌﻠﻤﻚ، ﻭﺃﺳﺘﻘﺪﺭﻙ ﺑﻘﺪﺭﺗﻚ،

ﻭﺃﺳﺄﻟﻚ ﻣﻦ ﻓﻀﻠﻚ ﺍﻟﻌﻈﻴﻢ ﻓﺈﻧﻚ ﺗﻘﺪﺭ ﻭﻻ ﺃﻗﺪﺭ، ﻭﺗﻌﻠﻢ

ﻭﻻ ﺃﻋﻠﻢ، ﻭﺃﻧﺖ ﻋﻼﻡ ﺍﻟﻐﻴﻮﺏ، ﺍﻟﻠﻬﻢ ﺇﻥ ﻛﻨﺖ ﺗﻌﻠﻢ ﺃﻥ

ﻫﺬﺍ ﺍﻻﻣﺮ nan Sai ka fadi irin bukatar ka da kake neman zabi a wajan Allah, Sai Kaci gaba da ﺧﻴﺮ ﻟﻲ ﻓﻲ ﺩﻳﻨﻲ

ﻭﻣﻌﺎﺷﻲ ﻭﻋﺎﻗﺒﺔ ﺃﻣﺮﻱ ﻓﺎﻗﺪﺭﻩ ﻟﻲ ﻭﻳﺴﺮﻩ ﻟﻲ ﺛﻢ ﺑﺎﺭﻙ

ﻟﻲ ﻓﻴﻪ، ﻭﺇﻥ ﻛﻨﺖ ﺗﻌﻠﻢ ﺃﻥ ﻫﺬﺍ ﺍﻻﻣﺮ ﺷﺮﻟﻲ ﻓﻲ ﺩﻳﻨﻲ

ﻭﻣﻌﺎﺷﻲ ﻭﻋﺎﻗﺒﺔ ﺃﻣﺮﻱ ﻓﺎﺻﺮﻓﻪ ﻋﻨﻲ ﻭﺍﺻﺮﻓﻨﻲ ﻋﻨﻪ

ﻭﺍﻗﺪﺭﻟﻲ ﺍﻟﺨﻴﺮ ﺣﻴﺚ ﻛﺎﻥ ﺛﻢ ﺭﺿﻨﻲ ﺑﻪ)

Bayan nan Sai kayi sallama, shikenan.




Anso in kayi ka kara maimaitawa gwargwadan yadda Kasamu iko.




ME zan gani idan nayi istihara??




Baka ganin komai sai abinda Allah yaso, Amma idan kayi to yadda zaka gane alkairi ne ko ba alkairi bane shine, (idan alkairi ne zakaji son abun ya karu a zuciyar ka, Dan haka sai ka kara himma wajan aikatawa, idan Kuma ba alkairi bane sai kaji son abun yana raguwa a zuciyar ka daga nan Sai Kai kokari barin abun.)




Addu'ar da zakai a mataki na 2 shine idan ka gane alkairi ne to kara neman taimakon Allah Akan yabaka cikin sauki.




Kayi sallah raka'a 2 kowace raka'a fatiha 1 kulhuwallahu 3 bayan kayi sallama sai kasake sujjada kayi kirari ga Allah kayi salatin Annabi saw sannan ka karanta (LA ILAHA ILLA ANTA SUBHANAKA INNEE KUNTA MINAZZALIMEEN) sau 41 sannan kafadi bukatar ka (ka roki abinda kake so) sannan ka sake salatin Annabi saw.




Ka tsarkake zuciyar ka lallai zakasha mamaki.




Allah shi yace aroke shi zai amsa.

Post a Comment

Previous Post Next Post

HTML/ JavaScript