AMFANIN 'YA'YAN MAGARYA DA KUMA GANYENTA


 

 WASU DAGA AMFANIN 'YA'YAN MAGARYA DA KUMA GANYENTA


A turance ana kiranta "Ziziphus abyssinica".

 Tarihi ya nuna amfara amfani da MAGARYA da kuma ganyenta tun kafin zuwan Addinin musulunci a larabce ana kiran iccen magarya "ASSIDIR" bayan zuwan addinin musulunci malamai da masana magunguna suka bada fatawar cewa za'a iya amfani da magarya domin magance da yawa daga cikin cututukkan yau da kullum.


Haka yake wajen turawa sunyi bakin binciken su basu kididdige alfanun magarya saidai suka kawo kadan daga abinda suka sani, domin sau dayawa dama maganin da bature ke amfani dashi itacen mune wasu ma a yankunan turawan babusu mu kuma cikin tausayi na ubangiji sai yabamu amma kuma mun dakile kanmu wajen sanin alfanunsu.


yadda ake sarrafata zuwa magani.


1.Ganyen magarya yana tsaftace jini domin yana dauke da sanadarin kashe kwayoyin cuta masu shiga jiki musamman mace lokacin da tagama al'ada (menstruation) wannan yasa ake son mace lokacin da tagama al'ada ta tafasa ganye magarya tana tsarki da ruwa akalla kwanaki 3 a jare.


2.Garin magarya kuwa mace ko namiji zasu iya amfani dashi suna sha a nono domin magance matsalar gyambon ciki wato (ulcer).


3.Domin magance matsalar sanyi na mata (infection) musamman zubar ruwa a gaban mace sanadin wannan sanyin asamu ganyen zogale, bagaruwar hausa, sauyar zogale, a hada da karamfani a tafasa ana zama acikin ruwan.

0/Post a Comment/Comments