Yadda Ake Yin Awara



ABUBUWAN BUKATA


  • Waken soya(yadda ake bukata)
  • Ruwan tsami/alum
  • Kayan miya
  • Maggi(ajino moto)
  • Mangyada

Za'a gyara waken soyar a wanke tas, sai akai a nik'a. Idan an dawo nik'a, sai ad'iga manja saboda yayi saurin fita a kyallen tatar.


Sai a dora tukunyar k'arfe(Saboda baya yin k'auri idan tukunyar karfe ce)

Sai a dora akan wuta adafa. Za'a tanadi ruwan tsami/alum yana fara tausa sai arik'a zuba ruwan tsamin/alum ahankali gefe da gefe, da tsakiya, za'a ga yana curewa, ruwa mai shar-shar na taruwa barayi guda, Sai a samu buhu wanda aka yaga, a sanya cikin roba ko kwano mai fad'i. Sai arika kwaso wannan dunk'ulalliyar awarar àna zubawa cikin buhun.Ruwan zai ta fita.Dama an jajjaga kayan miya, sai azuba maggi (fari kamar vedan ko ajino moto)da dan gishiri,sai a cakud'a, sannan a zuba cikin awarar ajujjuya su had'e. Sai adaure buhun a ajiye a gefe guda, kan wani abu yadda ruwan zai fita tas, idan ya tsane tsaf, sai a kwance a yayyanka a soya. Bayan an soya. Sai adiba wanda za'ayi  *cloud Awara dashi)


 Sai a kad'a kwai(kada akada sosai ya tsinke)


  •  Sai ayayyanka
  • Jar tattasai
  • Koren tattasai
  • Albasa
  • Yankan da dan tsayi(slice)

Sai azuba cikin Ruwan kwain adan juya, a sanya Magi(kalar da ake bukata) daidai misali. Idan kwai guda hudu ne, sai a sanya magi guda daya,fulawa rabin karamin cokali(1 tea spoon) a jujjuya (saboda zaifi kama awarar)

Sannan a rarraba soyayyar awarar biyu-biyu, azuba su cikin ruwan kwai a jujjuya.

Za'a d'ora mangyada a wuta idan yayi zafi,sai a zuba awarar nan da aka sanya cikin ruwan kwain  da aka yanka kayan miyar. Za'a ga yayi fuu! ya rufe awarar, sai bari har kwain ya danyi(golden brown)Sannan a kwashe a zuba a matsani, man ya tsane. Shikenan.


Note.Idan babu ruwan tsami za'a iya amfani da dan tsami/alumun

Idan mai tsome za'ayi (sai adafa farin magin da dan gishiri,idan ya huce, bayan an yayyanka awarar sai arika tsomawa ana soyawa.

Idan an zo soyawar da kwai kada acika wuta, kwain zai k'one.

Join our WhatsApp Group, to get latest news everyday,  join  WhatsApp Group 1

Subscribe to telegram channel toget latest update always Daily_net_news 

0/Post a Comment/Comments