AMFANIN MAN ZAITUN GA DAN ADAM

 


 ZAITUN DA MAN ZAITUN

Shidai zaitun itaciyace mai albarka da kuma bada cikakkiyar lafiya a jikin dan Adam , kamar yadda muka sani cewa zaitun abune mai daraja, kamar yadda muka samu bayaninta acikin ALKUR'ANI MAI GIRMA


haka kuma kamar yadda aka samu daga hadisan *Manzon Allah (ï·º)an karbo daga sayyadina umar yana cewa Manzon Allah (ï·º)* yace kuyi abinci da man zaitun kuma Ku shafashi ajikinku, domin hakika shi yana daga acikin bishiya mai albarka.

 tirmizi ne ya ruwaito


DAGA CIKIN AIKIN  ZAITUN


KARFIN MAZAKUTA

Duk mutumin da ya samu kanshi a wannan hali, to ya samu garin habbatussauda ya dinga zubawa acikin ruwan danyan kwai sannan a Soya shi da man zaitun ya dinga ci. Kullum , insha Allah zai samu karfin mazakuta sosai


Kada ka gaji duk wani magani da kagani ka gwada zaka dace insha Allah


CIWON CIKI

 Duk mutumin da yake ciwon ciki sai ya samu man zaitun kamar cikin cokali ya hada da garin habbatussauda ya cakuda ya sha safe da yamma.


Yasamu kamar sati daya yana sha ko kina sha insha Allah


CIWON KAI

 Duk mutumin da yake ciwon Kai to sai ya samu man zaitun yana shafawa a kansa yana kuma shan cokali daya da safe da Rana da dare insha Allah zai samu lafiya.


CIWON HAKORI

 duk mutumin da yake ciwon hakori sai ya samo ganya zaitun da ya'yan habbatussauda ya sakasu acikin garwashi ya buda bakinsa hayakin ya dinga shiga, insha Allah.


CIWON HANTA 

duk mutumin da ya kamu da wannan ciwo sai ya dinga shan manzaitun cikin cokali daya da safe daya da Rana daya da dare.


CIWON DADASHI

Duk mutumin da yake ciwon dasashi sai ya samu man zaitun ya dinga wanke bakinsa da shi.


CIWON SUKARI

duk mutumin da ya kamu da ciwon sikari to sai ya samu man zaitun da tsamiya yana hadawa yana sha kafin ya kwanta bacci insha Allah

Kubiyomu ta WhatsApp channel Daily Net News Don samun labarai Akai Akai: 

0/Post a Comment/Comments

Breaking News

Ads1

{ads}

Ads2