KARANTA HANYOYIN DA ZAKI BI DOMIN KI MALLAKE ZUCIYAR MIJINKI / SAURAYINKI
1_ Idan kina tare da saurayinki Kada ki kuskura wani abu mai kama da wari ya fita daga jikinki duk wata gaba da kikasan zata fitar da wari ki tabbata da kin tsaftace ta domin maza mun tsani wari saboda yana haifar da tsana
2_ Ki zamto ma abociyar kamshi amma ba ina nufin kiyi ta lafta turarurruka ba a a saisa saisa yadda dai wari bazai fita ba sai kamshi domin kamshin na kara dankon soyayya
3_ Ki zamto mai tsafta yadda dukkan tufafin da zaki saka a kodayushe ya ganki fes fes domin tsafta tana daga cikin yankin imani
4_ Ki zamto mai yawan yafiya idan sabani ya shiga tsakaninku domin harshe da hakori ma ana samun sabani watarana
5_ Ki guji rokon abin hannunsa domin roko yana jawo zubewar mutunci
6_ ki zamto mai rike gaskiya da aikatata domin rike gaskiya yana kawo aminta da juna
7_ Duk kankantar laipi kada kiyi girman kai idan takama ki bashi hakuri a zahirance ko waya ko ta hanyar tura sako domin ance durkusawa wada ba gajiyawa bane
8_ Kada ki zamto mai daukar zugar kawaye domin wata kawar bakinciki takeyi bata samu kamarsa ba
9_ Ki zamto mai yawan kulawa agreshi ta hanyar kiranshi ko flashing da tura sako a kalla koda sau 1 ne a rana domin mu maza muna mutukar bukatar kulawarku
10_ Kiyi kokari ki toshe duk wata hanya da kikasan zata iya bawa makiyanku kofa su kai suka suka ga abin kaunarki domin yawan kai zuga daga magulmata yana kawo farraqu na masoya
11_ Aduk lokacin da yayi miki laipi kada kice zakiyita fushi dashi batare da kin fadamasa laipinsa ba domin kin bayyana masa laipinsa zai saka yayita maimaita laipine batare da ya sani ba
12_ Ki zamto mai yawan godiya da nuna farinciki aduk lokacin da yayi miki kyauta duk kankantarta domin bayyanar farinciki a fuskarki na kara mishi azama gurin kyautata miki
A MATSAYINKI NA YA MACE INHAR KIN BI KO KIN KIYAYE WASU DAGA CIKIN ABUBUWAN NAN TABBAS ZAKI JUYA SAURAYINKI TAMKAR YADDA AKE JUYA WAINA
ALLAH YA HADAMU DA MASOYAN GASKIYA
Follow the Daily Net News channel on WhatsApp:
Post a Comment