Yadda Zaka Burge Mace Har Ku Fara Soyayya

 




Yadda Zaka Burge Mace  Har Ku Fara Soyayya

1. Iya bada labari: kazama ka iya bada labari masu Jan hankali, idan ka iya bada labari Mai Jan hankali, kasamu Dama cikin damarmakin da mace take baiwa Namiji wajen fara soyayya da ita.

2. Kamshi: yazama kana yawan amfanin da turare ko da yaushe, zama cikin kamshi Koda yaushe Yanasa mace tazama tanason zama dakai. Kuma bawai Ina nufin kake wanka da ruwan turare ba ko da yaushe, kana Saka turare da yawuce misaliba, daidai misali nake nufi, duk Wanda ya matso kusa dakai yasan kana cikin kamshi.

3. Wayo: Bawai Ina nufin wayon zama na mutum dabanba! Abun nufi shine kana Bata labari ko Hira kar yazama hirarka akan Abu daya kakeyi kullum, Hakan zai sa tatsaneka saboda hirarka akan Abu daya kake kullum, kake kawo Mata Hira akan zamantakewar rayuwa da shawarwari da Abubuwan makamantan haka.


4. Yadda kake sa kaya: Bai kamata kake Saka kowane irin kaya kana zuwa wajen maceba, misali kamar Maza masu yin kwallo, Wasu sunason yawo da kayan kwallo, ko dogowar Riga kawai, Mata sunfi so kake shiga ta mutunci.

5. Kiyaye abunda takeso: Dan Adam an halicceshi da son abubuwan daban daban, abunda Wani yake so Kai bakaso, sai Ka kiyaye abunda takeso, kar kabari abunda take so yazama abun kushewa awajenka.

6.karamci: mace tanason Mai karamci, kazama Mai karrama kowa, ba iya yarinyar dake tare da itaba, ita zuciya tanason Wanda yake karramata.

7. Karya: kar kazama Mai karya, karya Yana sa aki mutum ko wayene shi, idan ya kasance ta shaideka da yin karya, zaka iya rasa soyayyar ka agareta.

Don Allah ayimana sharing.

Allah yasa mu dace. Ameen



0/Post a Comment/Comments

Breaking News

Ads1

{ads}

Ads2