Ma’aikatar Noma Da Samar Da Abinci ta Tarayya Za Ta Ƙayyade Farashin Abinci A Najeriya, -Ministan Noma


 Ma’aikatar Noma Da Samar Da Abinci ta Tarayya A Ƙarƙashin Jagorancin Mai Girma Ministan Noma, Sanata Abubakar Kyari (CON) Za Ta Ƙayyade Farashin Abinci A Najeriya, -Ministan Noma 


Mai girma ministan yaɗa labarai da wayar da kan al'umma, Alhaji Muhammad Idris Maagi, yayi taro da manema labarai domin bayyanawa ƴan Najeriya cigaban da ake samu dangane da ayyukan da gwamnatin take gudanarwa a ƙasa.


Sen. Abubakar Kyari CON, a matsayinsa na baƙo mai jawabi, ya yi tsokaci kan ƙalubalen da ƙasa take fuskanta a fannin noma, matsalar samar da amfanin gona da ƙarancin ƙasar noma da tasirin ƙarancin kayayyaki da yawan buƙatarsu da tsadarsu wanda zai kai ga sanya dokar ta-ɓaci.


Ya ƙara da bayyana matakan da gwamnati ta ke ɗauka domin samar da wadataccen abinci a ƙasa kamar haka:


1. Anyi wa manoma rijista kan tsarin noman rani ta tallafin NAGS-AP, AFDB na kashi 50 cikin dari na kayan noma da kuma irin alkama a kyauta, inda sukayi noma kimanin hekta 120,000, a shekarar da ta gabata. wanda aka yi a Jihar Jigawa.


2. Gwamnati ta ɗauki matakan tabbatar da an tantance manoma na gaske wanda gwamnatin Jiha za ta tantance su domin ka da ƴan siyasa waɗanda ba manoma ba su shiga cikin shirin da za’ayi a gaba. 


3. Za a noma hekta 150,000 ƙarƙashin shirin noman shinkafa, masara da rogo inda za a shigar da kimanin manoma 300,000.


4. Za a samar da tallafi daga ƙungiyoyin ba da agaji na Duniya domin sauƙaƙa farashi, sannan gwamnati zata bada ƙarin tallafi wa manoman da basuda halin biyan kudin karbar kayan noma.


5. Za a ɗauki matakan tantance masu fitar da abinci ƙasar waje a kan iyakokin ƙasa domin daƙile masu safararsa ba bisa ƙa'ida ba. Fitar da abinci waje yana amfanar da ƙasa, amma yana zama illa idan gwamnati ba ta amfanar komai daga ciki.


6. Ma'aikatar aikin gona ta buƙaci fitar da hatsi tan 42,000 domin rabawa ga masu ƙaramin ƙarfi don rage matsalar hauhawar farashin abinci da ƙarancinsa.


7. Za a zamanantar da harkar noma domin ƙara yawan abincin da ake samarwa da gujewa hasararsa bayan an girbe.


8. Za a samar da shirin (Green Imperatives) wanda zai laƙume biliyoyin daloli domin samar da cibiyoyin kula da aikin noma a dukkan ƙananan hukumomi 774 na Najeriya. Tsarin zai taimaka wajen samar da kayan aiki na haya a farashi mai sauƙi.


9. Za a tabbatar da cewa an raba tan 42,000 na hatsi cikin adalci domin ya je hannun waɗanda suka kamata ta hanyar yin amfani da hukumar ba da agajin gaggawa ta ƙasa, (NEMA) da hukumar tsaron farin kaya (DSS), domin ba da bayanai na haƙiƙa game da kowacce shiyya da ake buƙata.


10. Za a samar da hukumar saye amfanin gona wacce za ta jagoranci ƙayyade farashin kayan abinci a kasuwa da kare manoma daga tafka hasara yayin ambaliya. Hukumar za ta na sayen abinci daga manoma tana sayar musu ga masu buƙata domin ganin ba a cuce su ba.


Minista Kyari ya ƙarƙare da cewa tuni gwamnati ta himmatu ainun wajen rage farashin kayan abinci suna kuma fatan haƙarsu za ta cimma ruwa. Yanzu haka farashin hatsi ya ragu a kasuwa.

0/Post a Comment/Comments

Breaking News

Ads1

{ads}

Ads2