![]() |
source: bbc hausa |
An kama saurayin wata mata, wadda ta kashe kanta, da laifin cin zarafi da wulaƙanta ta, amma an wanke shi daga zargin aikata kisa.
An gurfanar da Ryan Wellings, na yankin Lancashire a Birtaniya ne gaban kotu bisa zargin shi da kashe abokiyar zamansa, Kiena Dawes, wadda ta kashe kanta sanadiyyar cin zarafi.
Wellings bai yi ko gezau ba a lokacin da kotu ta wanke shi daga zargin na kisa.
Sai dai Æ´ar’uwar marigayiya Dawes ta fashe da kuka a lokacin da aka sanar da hukuncin.
Shi kuwa Wellings ya yi murmushi sannan ya sumbaci budurwarsa a lokacin da za a fitar da shi daga kotun, domin nuna farin ciki.
An tuhumi Wellings da aikata kisan kai ne bayan abokiyar zamansa ta kashe kanta inda ta bar rubutaccen saÆ™o cewa: “An kashe ni ne” ta Æ™ara da cewa Wellings ne “ya kashe ni”.
An haƙƙaƙe cewa ta rubuta saƙon ne gabanin ta kashe kanta a ranar 22 ga watan Yulin 2022.
Alƙalai sun saurari ƙorafin da ya nuna cewa Kiena Dawes ta shafe shekara biyu tana fuskantar cin zarafi a hannun WellingsAsalin hoton,Family handout
Bayanan hoto,Alƙalai sun saurari ƙorafin da ya nuna cewa Kiena Dawes ta shafe shekara biyu tana fuskantar cin zarafi a hannun Wellings
Marigayiya Dawes ta haÉ—u da Wellings ne a watan Janairun 2020, inda suka fara soyayya nan take.
Cikin mako ɗaya bayan haɗuwarsu, Dawes - wanda a baya aka taɓa kamawa da laifin cin zarafin abokiyar zamansa - ya sa an zana masa suna da fuskar sabuwar masoyiyarsa Dawes a jikinsa.
Haka nan ya yi mata alƙawarin aure a cikin wata uku.
Sai dai bayan sun fara zama tare, Dawes ta ce “mafarkinta mai daÉ—i” ya koma “mafarkin tashin hankali”, kasancewar Wellings mutum ne mai saurin zuciya kuma yana yawan shaÆ™ar hodar iblis da kuma kwankwaÉ—ar barasa.
Cikin abubuwan da ya riƙa yi mata har da mari a kai-a kai, da jan gashin kanta, da kuma barazanar karya mata haƙora, kamar yadda aka shaida wa alƙali.
Wellings ya yi mata tabo a fuska a lokacin da ta samu ciki, inda ya riƙa sukar ƙibar da ta yi, sannan ya riƙa bin karuwai a shafukan sada zumunta.
Ana sa ran yanke wa Wellings hukunci a ranar 16 ga watan Janairu.
source: bbc hausa
Post a Comment