Tsohuwar Budurwar Bilal Villa Ta Magantu Kan Bidiyon Batsa da Ke Yawo



Tsohuwar budurwar shahararren mawakin Arewa, Bilal Villa — Amani — ta karyata zargin cewa ita ce ake nunawa a bidiyon batsa da ke yawo a kafafen sada zumunta.


Amani ta bayyana cewa matar da ke cikin bidiyon tana amfani da kayan kwalliya na farata da kuma nau’in jan baki da ita kuma ba ta taba amfani da su ba. Saboda haka, ta ce babu wani abu da ya yi kama da ita a bidiyon.


Ta bayyana cewa duk wanda ya ce ita ce a bidiyon kawai yana yada karya da sharri, kuma hakan ta ce bata yarda da shi ba ko kadan.


A cikin kalamanta ta ce:


“Na ga wani bidiyo a shafukan sada zumunta suna cewa ni ce aka fallasa. Ina so in bayyana muku cewa ba ni bace a cikin bidiyon, ko ku yarda ko kada ku yarda. Kuma wallahi ban yafe wa masu yada wannan kazafin ba.”


A ƙarshe, Amani ta sake nanata cewa ba ta yafe wa masu yaɗa wannan ƙarya ba domin ya cutar da sunanta da martabarta.


0/Post a Comment/Comments