Wani Matashi Ya Kwaikwayi Salon Sarkin Mota Ya Haskaka Kansa a Sabon Bidiyon Barkwanci


 

A cikin wani sabon bidiyon da ke ta yawo a kafafen sada zumunta, wani matashi ya yi amfani da shahararren salon tallan Sarkin Mota—wanda aka saba gani yana nuna motoci cikin nishadi—domin shirya nasa bidiyon barkwanci mai matuÆ™ar kayatarwa.

Matashin ya yi kwaikwayon yadda Sarkin Mota ke gabatar da kaya, amma wannan karon ba mota ya nuna ba… sai dai “motar gidansa” wato matarsa!

Ya bayyana cikin bidiyon cewa matar tasa itama ta kware wajen amfani da fasaha, saboda yana iya sarrafata da “remote control”. Wannan kalamai nasa sun sa jama’a dariya, tare da ganin yadda ya yi wakiltar salon Sarkin Mota cikin hikima da ban dariya.

A daren bidiyon, ya nuna matarsa yana cewa: “Ga irin wannan mota nan… Sarkin Mota ba shi da ita!” Wani abin dariya shi ne yadda ya Æ™ara da cewa ba zai yiwu Sarkin Mota ya mallaki irin wannan “mota” ba, domin kamar yadda ake yadawa, shahararren mai tallar motoci É—in gwauro ne Æ™warai.

https://x.com/EngrAdamz/status/1995292995361579150?t=9AFAIUvDux_PXg1ILyIrpw&s=19

Bidiyon ya ci gaba da jawo hankalin jama’a saboda yadda ya haÉ—a barkwanci, kirkira, da kwaikwayo cikin salo mai tsafta da ban sha’awa. A comment section dai, mutane na ta bada ra’ayoyi tare da jiran ganin cikakken bidiyon da marubucin ya yi alÆ™awarin dora musu.



0/Post a Comment/Comments