Wani sabon faifan bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta ya tayar da muhawara, inda aka hango wani mutumi a daji – wanda wasu ke zaton É—aya ne daga masu garkuwa da mutane – yana bayyana murna kan nadin sabon Ministan Tsaro, Christer Musa.
A cikin bidiyon, mutumin ya yi wasu kalamai masu ban mamaki da suka sa jama'a da dama tambayar ainihin manufarsa. Duk da cewa ba a tabbatar da sahihancin bidiyon ko ainihin mutumin ba, hakan bai hana jama’a yin martani ba, musamman ganin yadda lamarin ya zo a daidai lokacin da ake Æ™ara matsa kaimi kan tsaro a fadin Æ™asar.Herdsman congratulates Gen. Christopher Musa on his appointment as the new Minister of Defence🫣pic.twitter.com/zuKxsesfrH
— Instablog9ja (@instablog9ja) December 4, 2025
Masu lura da al’umma sun yi kira da a kula wajen É—aukar irin waÉ—annan bidiyoyi, domin galibi ana yawan samun bidiyoyi na bogi da ake yadawa ba tare da hujja ba.

Post a Comment