YIN WANKA KULLUM YANA CUTAR DA FATAR DAN ADAM


YIN WANKA KULLUM YANA CUTAR DA FATAR DAN ADAM



Binkicen da likitan fata DrJoshua Zeichner dan kasar amurka yayi ya tabbatar da cewa kusan kowane dan Adam a kullum yana wanka sau daya ko sau biyu. Ya kara da cewa yin wanka kullum yana cutar da dan Adam fiye da yadda yake tsammani.




Yin wanka da ruwa mai zafi yana cire wasu kwayoyin halitto na bacteria wadanda suke taimakawa gurin kare fatar bil adama daga wasu cutuka, hakanan yin wanka da ruwa mai zafi yana busar da fata tare da bude hanyoyin da cutuka zasu iya shiga.




Hakanan wani likitan fata din Dr George Moncrieff wanda malami ne a jami'ar oxford ya kara da cewa mutum yayi iyakar kokarin ganin cewa ya kiyaye fatar sa daga wanda da sabulu, shiyasa a cewar sa shekarar sa fiye da ashirin a rayuwarsa baya wanka da sabulu.




A cewar Dr George Moncrieff sinadaran da ake amfani dasu gurin yin sabulan da muke amfani dasu na wanka, suna cutar da fata fiye da kyaran da suke mata. Hakanan yawan wanka da sabulu yana sawa fata ta tsufa sosai, da za'a dauko wanda yayi shekara goma baya wanka da sabulu da wanda yayi shekara goma yana wanka da sabulu, toh fatan wanda yake wanka da sabulu sai tafi nuna tsufa.




Gamayyar likitocin fata na duniya sun tabbatar da cewa yin wanka sau daya a cikin kwana uku ya ishi dan adam. Shima din wasu likitocin na ganin cewar idan ba fata dayi dattin da lallai sai an wanke ta da sabulu ba toh kada a saka mata. Manyan models na duniya da ake saka hotunan su a talla da yawa basa amfani da sabulu gurin wanka.




Wallahu Ya'alamu.....




Author: Muhammad Abdulrahman Sheka

0/Post a Comment/Comments

Breaking News

Ads1

{ads}

Ads2