KO GOBNATI TA ƊAUKI MATAKIN RUFE MANHAJAR TIKTOK KAMAR YADDA TA RUFE TWITTER DON SUN SOKI MANUFAR GOBNATI KO SHUGABAN ƘASA KO ALLAH YAI FUSHI DA ƘASAR.
KO KASAN WANNAN BAYANIN KO DALILI A GAME DA ƘIRƘIRAR MANHAJAR TIKTOK?
DA AKA TSANANTA BINCIKE AN GANO CEWA MANHAJAR TIKTOK NADA ALAƘA DA MASU SHAREWA SHAIƊAN HANYA WATO (ILLUMINATI)
GA CIKAKKEN BINCIKE GAME DA MANHAJAR TITTOK ILLA, MUMMUNAR MUNUFA, TARE DA HAUKATA MATASA A DUNIYA
Da farko dai ita wannan manhajar ta TITTOK ko DOUYIN da harshen Sin wato (China) wani shahararren kamfanin rawa da wake ne ya ƙirƙire shi mai suna ByteDance na wani matashi mai suna Zhang Yiming mai shekaru 38 ɗan asalin ƙasar ta Sin a shekara ta 2016 amma sai a shekara ta 2017 aka ƙaddamar da shi inda ake ɗora bidiyo mai tsawon daga daƙika 15 zuwa mintina 3 inda aka zuba masa harsuna wato (Language) sama a 40 sannan ita wannan manhajar ta samu ƙarbuwa sosai wanda idan ka kwatanta ta da sauran kafafen sada zumunta babu wadda ta karɓu kamar ta domin cikin lokaci ƙalilan da ƙaddamar war sama da mutane miliyan 300 sauki rijista inda a yanzu a kullum ake kallon bidiyo daban-daban har sama da mutane biliyan ɗaya
Inda gizo ke saƙar ya kamata kusani shi wancan matashin mai manhajar TITTOK mai suna Zhang Yiming kwantiragi ya ɗauki domin lalata tarbiyyar da rayuwar al'umma musamman matasa da tallata fasikanci, fajirci, da yaɗa su a faɗin duniya? Kuma sun fara yin nasara ko kasan gwamnatin sa ta ƙasar Sin suna samun kuɗin shiga mai yawan gaske amma kuma suna da ƙaida akan matasan su idan kai bidiyo ya haura ƙaidar za'a ɗaure mutum? Kuma yanzu su dakatar da amfani da manhajar ko kasan shima wannan matashin mai manhajar ba cikakken hankali gareshi ba? Ko kasan daga fara amfani da wannan manhajar matasa da dama sun zama fitsarirru, marassa mutunci, rashin kunya, fidda tsiraici, faɗa da zage-zage, cin mutuncin mutane, tallata fasiƙanci da fajirci da dai saura munanan ɗabiu kala-kala.
Idan kunne ya ji jiki........ A yanzu haka ƙasashe kamar su India, Pakistan, USA, Bangladesh, Indonesia da sauransu duk su haramta amfani da wannan shaiɗaniyar manhajar, cikin wannan shekarar sai da gwamnatin kasar Masar (Egypt) ta daure yawa matashiya mai shekaru 20 da haihuwa mai suna Haneen Hossam har shekaru 10 saboda tana koyawa matasa amfani da wannan mummunan manhajar ta TITTOK saboda su tuni suka gano zaai musu sakiyar da ba ruwa domin idan aka lalata tarbiyyar matasa a kowace ƙasace to an kashe wannan ƙasar kuma muma matasa ya kamata mu riƙa bincika abu kafin mu fara amfani da shi. Allah shirya mu kan hanya madaidaiciya.
Domin a maauni na amfani da cutarwa ga ita wannan manhajar to cutarwar tafi yawa sosai fiye da amfanin ta don haka ya kamata a dauki matakin kauda ita. Akwai bayanai munana akan manhajar TITTOK amma idan hali yayi zamu fito da su.
Daga: Muhammad lawan Abubakar
Post a Comment