Maganin kurajen gaba da kaikayin gaba.
Kai
tsaye ana cewa sanyin mara shine yake jawo wannan matsala,amma abinda
ya kamata mu sani shine ba iya shi kadai yake jawowa ba akwai abubuwa da
dama.
Akwai abubuwa da yawa da ke haifar da
wannan matsala, bayan kamuwa da cuta da akan ce yana haifar da wannan
matsalar, akwai wasu abubuwa a bayansa.
Wani
lokacin sanya kaya ko underwear wanda ya matse ka yana jawo kaikai wani
kuma motsa jiki ko tafiya mai nisa a kafa ko gudu suna jawo masa wannan.
Akwai
karancin tsafta, mutum ya rika sanya underwear kusan mako guda ba tare
da an canza shi ba, wasu kuma ba sa barin shi ya bushe bayan sun yi
wanka sannan su sanya tufafi, duk suna haifar da wannan matsala.
Koda gaban dadewa yake yana saba yana wari insha Allah idan akai wannan zaa samu waraka
Abubuwan da ake buƙata:
1. Man Darbejiya
2. Man tafarnuwa.
3. Man zogale.
4. Man kwakwa.
Yadda ake hadawa:
Da
farko zaka samu kowanne daga cikinsu, amma ka tabbata ka samu na asali
masu kyau saboda biyan bukata, kuma kowanne yana samuwa a Islamic
chemist.
Idan ka saya kowanne, auna shi da murfin kwalban.
Sai
a hada su waje daya a shafa a wurin da pimples ya bayyana ga namiji,
idan ya takura sai a bar shi, sai a yi wanka a bar shi ya bushe, sai a
shafa wannan maganin a wurin sannan a sa tufafi. , sannan a yi kokarin
canza rigar a kowane kwana 2. .
Idan mace tana
da kuraje ko kamuwa da cuta na dogon lokaci ko kamuwa da cuta, sai ta
sami auduga ta shafa mai a jikinta. Zata kwanta ta danna gabanta. kuma a
sha ruwan dumi, a guji shan ruwan sanyi.
Allah yasa mu dace.
Kuturawa yan uwa da abokai wannan hadin mai tarin amfani ta WhatsApp
Post a Comment