Fitaccen mawakin Najeriya mai lashe lambar yabo ta Grammy, Damini Ogulu, wanda aka fi sani da Burna Boy, ya bayyana dalilin da ya sa ya sauya daga addinin Kiristanci zuwa Musulunci, inda ya ce wannan canjin wani ɓangare ne na neman hasken ruhaniya da zurfin fahimtar rayuwa.
A wata tattaunawa da ya yi kwanan nan da mai watsa shirye-shirye Playboymax, Burna Boy ya ce neman zurfin ma’ana ta hanyar nazarin addinai daban-daban ya bar shi cikin ruɗani maimakon samun amsar da yake nema.
“Tun ina ƙarami, Kirista ne ni sannan daga baya na koma Musulmi. Kamar na karanci komai, amma har yanzu ina ƙoƙarin gano me ke faruwa a gaske, ka gane? Maimakon in samu haske, bincike yana ƙara mini ruɗani,” in ji shi.
Mawakin ‘City Boys’ ya ƙara da cewa tafiyarsa ta ruhaniya tana ci gaba, domin har yanzu yana neman gaskiyar kansa da fahimta fiye da iyakokin addinai da aka tsara.
Wannan bayani nasa ya zo watanni bayan wani mawaki ɗan Najeriya, 9ice, ya yi magana kan nasa sauyin ruhaniya.
Mawakin ‘Gongo Aso’ ya bayyana cewa ya koma ga addinin gargajiya na Ifa bayan wani “hari na ruhaniya” da ya sa ya kwanta rashin lafiya har tsawon watanni shida.
A wata hira da Nancy Isime da ta bazu a kafafen sada zumunta, 9ice ya ce yana so da tun farko ya rungumi addinin gargajiya, inda ya bayyana wannan sauyi a matsayin abin da ya canza masa rayuwa ƙwarai.
Daga: jaridar leadership

Post a Comment