Tsirrin habbatussauda da Dabino ga Lafiyar ya mace gun samar da Ni’ima da samun gamsuwar ma'aurata




Habbatussauda na taimakawa mata wajen inganta lafiyar jiki da jin daɗin zamantakewar aure. Musanman habbatus saudah da dabino, waɗanda aka dade ana amfani da su a al’adance.

1. Habbatussauda nah Ƙara Ni’ima da Yawan Ruwa

Dabino na ƙunshe da sinadarai masu taimakawa jiki wajen samun kuzari da motsa sinadaran sha’awa.

Habbatus saudah kuma na taimakawa wajen tsaftace jiki da kuma inganta lafiyar mahaifa, wanda hakan kan taimaka wa mace ta ji sauƙi da walwala.

2. Habbatussauda Na Daidaita Sinadaran Hormone

Mata da ke fama da bushewa ko raguwar sha’awa na iya amfana da wannan haɗi, domin yana taimakawa wajen daidaita sinadaran hormone da jiki ke buƙata.

3. Inganta Jini da Ƙarfi

Idan jini yana gudana yadda ya kamata a jiki, mace na samun ƙarin kuzari da natsuwa. Dabino da habbatus saudah na taimakawa wajen inganta wannan yanayi.

4. Rage Bushewa da Rashin Jin Daɗi

Haɗin na taimakawa wajen rage bushewar gaba da kuma ƙara laushi, wanda ke taimakawa mace ta samu sauƙi a rayuwar aurenta.

Yadda za'a hada:

Habbatus saudah (ƙaramin cokali 1)

Dabino guda 3–5

Zuma (cokali 1)

Madara ko ruwa (zabi)

Hanyar hadawa:

A jika dabino na tsawon awa 4 ko daga dare zuwa safe.

A cire ƙwallayen dabino, a markada shi tare da habbatus saudah da zuma.

A sha da safe kafin cin abinci ko da dare kafin kwanciya.

Ana iya amfani da shi na tsawon makonni 2–3 domin samun biyan bukata.


Join Our WhatsApp Group

Don’t miss out on any real-time information. Join our WhatsApp group to stay updated



0/Post a Comment/Comments